Featured
Kungiyar Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai Ta Janye Dakatarwar Da Tayi Kan Shiga Lamuran Gwamnatin Kano
Kungiya wakilan kafafen yada labarai dake aiki a jihar Kano ta dage dakatarwar da tayi na shiga harkokin gwamnatin jihar.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Aminu Ahmed Garko ya fitar, jim kadan bayan taron gaggawa da mambobin kungiyar suka gudanar a ranar Lahadi.
“Kungiyar wakilan kafafen yada labarai na jihar Kano karkashin kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya na sanar da al’umma cewa ta dage dakatarwar da ta yiwa shiga harkokin gwamnnatin jihar Kano nan take”, inji Aminu Garko.
Yayi bayanin cewa ‘yan kungiyar sun kauracewa shiga harkokin gwamnatin ne kan nuna rashin gamsuwar yadda ake halin ko in kula da lamarin ‘yan jarida.
Ya ce kungiyar ta lura cewa dakatarwar ta haifar da sakamakon da ba a bukata ga fannin yada labarai a yanayin tsaro da jihar ke ciki.
