Featured
Tinubu Zai Bar Birnin Legas Zuwa Afrika Ta Kudu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga birnin Legas zuwa Pretoria na Afrika ta kudu domin halartar bikin rantsar da shugaba Cyril Ramaphosa.
Za a rantsar da shugaba Ramaphosa ne bayan ya lashe zabe karo na 2.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban kasar zai dawo Najeriya a ranar Talata bayan kammala taron.
Shugaban kasa Tinubu dai na hutun bikin Sallah a yanzu haka a birnin Legas.
