Featured
Jam’iyyar APC Ta Buƙaci Jami’an Tsaro Su Kama Rabi’u Kwankwaso
Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana kalaman da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a matsayin abun takaici.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa gwamnatin tarayya.
Ya kuma ce jam’iyyar ta maka Kwankwaso a kotu domin a kama shi bisa zargin da ya yi na cewar gwamnatin tarayya na yin katsa-landan cikin harkokin Kano.
