Featured
Kasar Nijar ta soke lasisin kamfanin hako ma’adani na Faransa
Kasar Nijar ta soke lasisin kamfanin Orano na Faransa daga hako ma’adanin Uranium.
A cewar kamfanin a wani mataki da ya kara fito da tsamin alaka tsakanin sojojin dake mulki a Nijar da mahukuntar kasar Faransa.
Kamfanin na Orano ya ce an cire shi daga aikin hakar ma’adanai a Arewacin kasar inda ake hako ma’adanan da ake sarrafa makamakan kare dangi.
An fara aikin hakar ma’adanan nen tun a shekerar 2015 sai dai farashin Uranium yayi kasa a shekarar 2011 bayan hatsarin Makamin kare dangi na Japan.
Har yanzu dai kasar ta Nijar bata mayar da martani ba kan ikirarin kamfanin.
Sai dai ta sha alwashin bibiyar yarjejeniyar hakar ma’adanan.
