Featured
Gwamnatin tarayya za ta kafa kotun hukunta masu aikata laifuka a fannin wutar lantarki
Gwamnatin tarayya a jiya Alhamis ta ce tana shirin kafa kotun hukunta masu aikata laifuka a fannin wutar lantarki domin magance masu satar wutar a kasarnan.
Da yake jawabi a yayin taron manema labarai a birnin tarayya Abuja, shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta kasa, Aliyy Tahir ya ce suna shirin kafa kotun nan gaba.
Ya ce za a kafa kotun ne domin zukulo masu aikata laifuka a fannin wutar lantarki kuma za a sanarwa da majalisar wakilai shirin kafa kotun.
Ya ce da kotun ne za a magance ayyukan bata gari a fannin na samar da wutar lantarki.
