Featured
Sojojin Najeriya zasu kulla alaka da kafafen yada labarai don tabbatar da tsaron kasa
Rundunar sojan Najeriya ta bayyana shirinta na karfafa alaka da kafafen yada labarai domin tabbatar da tsaron kasa.
Rundunar sojan ta bayyana hakan ne a jiya Alhamis a wani taro da ya gudana a jihar Kano mai taken “Rundunar sojan Najeriya da alaka da kafafen yada labarai”.
Rundunar ta ce taron na daga cikin tarukanta na shekerar 2024.
Da yake jawabi a yayin taron, Manjo Janar Nosakhare Ugbo yayi bayani kan muhimmancin hada kai da aiki tare tsakanin rundunar sojan Najeriya da kafafen yada labarai.
