Featured
Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin Emefiele na Naira Biliyan 12
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin Legas ta bada umarnin kwace kadarori da kimarsu ta kai Naira Biliyan 12.18.
Kadarorin dai nada alaka da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN wato Godwin Emefiele.
Kotun ta bada umarnin kwace kadarorin ne bayan neman bukatar hakan da hukumar EFCC tayi.
A ranar 5 ga watan Yuni ne dai mai shari’a, Chukwujekwu Aneke, ya bada umarnin kwace kadarorin na wucin gadi.
Kadarorin dai suna a yankunan babban birnin tarayya Abuja.
Mai shari’ar ya umarci EFCC ta wallafa umarnin kotun a jarida ko da wani zai nuna rashin gamsuwa da karbe kadarorin.
