Featured
Bashin da ake bin Najeriya ya kai Tiriliyan 121 – NBS
Bashin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira Tiriliyan 97.34 a farkon shekarar 2023 zuwa Naira Tiriliyan 121.76 a watanni 4 na farkon shekerar 2024.
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ce ta bayyana hakan a rahotan bashin da ake bin Najeriya na gida da waje da ta fitar a birnin tarayya Abuja.
Rahotan ya ce bashin da ake bin gwamnatoci a Najeriya ya karu da kaso 24.99 kan idan aka kwantanta da farkon shekarar 2023 da 2024.
Ta ce bashin da ake bin Najeriya daga waje ya kai Naira Tiriliyan 56 a farkon shekerar 2024 a yayin da a cikin gida ake bin gwamnatoci bashin Naira Tiriliyan 65.65.
Haka kuma adadin bashin da ake bi daga wajen kasar ya kai kaso 46.05 a farkon shekerar da muke ciki sai bashin da ake bi a gida ya kai kaso 53.95.
A kididigar da hukumar ta fitar ta ce jihar Legas ce wacce aka fi bi bashin cikin gida wanda ya kai Biliyan 929.41 sai jihar Delta da ake bi bashin Biliyan 334.90.
Rahotan ya kuma nuna cewa jihar Jigawa ce wacce ba a bi bashi da yawa inda ake binfa Naira Biliyan 2.07 da jihar Ondo da ake bi biliyan 16.40.
