Featured
Gwamnatin Kano za ta dauki masu gadi dubu 17 a makarantun Firamare
Gwamnatin jihar Kano ta ce fitar da kudi Naira Biliyan 3 domin gina sabbin ajujuwa a makarantu a kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi bayanin hakan a jiya Talata yayin taron masu ruwa da tsaki a fannin ilimi na jihar Kano.
Ya ce aikin za a yi shi ne domin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa ga daliban jihar.
Abba Kabir Yusuf ya ce za a dauki ma’aikata dubu 17 da zasu yi gadin makarantun firamare inda kowacce karamar hukuma za a dau ma’aikata dari 4.
“Za a dau masu gadin ne a unguwannin da makarantun firamaren duke domin tabbatar da suna aikinsu yadda yakamata”, inji shi.
Ya ce kowacce karamar hukuma zata karbi Naira Miliyan 25 na gyaran makarantu inda hukumar kula da ilimin bai daya ta SUBEB za ta sanya idanu kan yadda ake gudanar da ayyukan.
