Featured
Za a turawa majalisa bukatar siyawa shugaban kasa da mataimakinsa sabbin jirage nan bada jimawa ba
Za a sanya kudin da za a siyawa shugaban kasa sabon jirgi a kwarya kwaryar kasafin kudi na shekarar 2024, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa za a mika bayanan yadda za a siyi jirgin ga majalisar wakilai nan bada jimawa ba.
A watan Afrilu ne dai, shugaban kasa Tinubu ya fasa hawa jirgin shugaban kasa bayan ya samun matsala a lokacin da zai ziyarci birnin Riyadh na Saudia.
Haka shi ma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima an gan shi a jirgin haya a yayin da ya isa jihar Ogun.
A don haka ne gwamnatin tarayya ta sanya gwanjon jiragen domin siyar dasu.
Kwamitoci biyu na majalisar wakilai sun bada shawarar siyawa shugaban kasar sabbin jirage guda biyu domin amfanin shugaban kasa da mataimakinsa.
