Featured
ACReSAL Za Ta Dasa Bishiyu Miliyan Uku A Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta hanyar shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL), ta kaddamar da shirin dashen Bishiyoyi miliyan uku domin magance sauyin yanayi da gurbacewar muhalli.
Kakaki24 ya ruwaito cewa, A yayin wani taron manema labarai a Kano ranar Juma’a, jami’in kula da shirin ACReSAL Dr. Dahiru Hashim, ya jaddada muhimmancin da ake bukata na magance sauyin yanayi da kuma gurbacewar muhalli a yankin.
Dr. Dahiru ya bayyana cewa shirin zai kawata jihar Kano da kuma kare muhallinta.
Ya ce shirin da aka yi wa lakabi da “Dasa Bishiyu Miliyan Uku (3MTP),” ayyukan ACReSAL ne suka yi shi da nufin magance sauyin yanayi, lalata muhalli, da sare itatuwa a yankin.
“Gwamna Abba Kabir-Yusuf, mai fafutukar tabbatar da dorewar muhalli, ya jaddada muhimmanci da kuma rawar da bishiyu ke takawa wajen tabbatar da daidaiton muhalli.
A cewarsa, ana kuma samar da matakan kafa doka don haramta da hukunta masu sare bishiyun babu gaira babu dalili.
“Kokarin da aka fara yi a karkashin shirin ya hada da dasa bishiyu 5,000 a kan muhimman hanyoyi kamar Titin Hadeja, da Titin Audu Bako da Titin Airport da Titin Sharada Ja’en da kuma wasu wajejen akan Titin Katsina.
“A cikin tsarin dashen bishiyun za a dasa miliyan biyu don farfado da gandun daji don taimakon manoma.
A karshe Jami’in gudanarwar aikin ya yi kira ga al’umma da su shiga wannan shiri mai cike da tarihi, tare da bayar da gudunmuwa wajen samar da yanayi mai inganci.
