Featured
Motar Tirele Ta Kashe Masallata 14 a Kano
A kalla mutane 14 suka rasa ransu a wani hatsarin mota a garin Imawa dake kan hanyar Zaria zuwa Kano a karamar hukumar Kura ta jihar Kano.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura na jihar, Ibrahim Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar hatsarin ga manema labarai a jiya Juma’a a Kano.
Ya ce lamarin ya faru ne yayin da wata babbar mota mai lambar MKA 537 XN ta kaucewa hanyarta inda ta fada kan masu Sallar Juma’a inda 14 daga cikinsu suka rasu.
Abdullahi ya ce “Mun samu kira da misalin karfe 1:50 na rana a ranar 28 ga watan Yuni, bayan samun bayanai nan take muka tura jami’an mu zuwa wurin da hatsarin ya faru.
” Hukumar FRSC ta himmatu wajen kare hadurra kuma muna kira ga al’umma da su dinga bin dokokin hanya”.
