Featured
Bauchi: Mutane 50 da ake zargin sun kamu da cutar Amai da Gudawa
Hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Bauchi, ta ce ta samu rahotan wadanda ake zargin sun kamu da cutar Amai da Gudawa 50 daga kananan hukumomi 3 na jihar daga watan Janairu zuwa yau.
Shugaban hukumar, Dakta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da bikin makwan kula da lafiyar yara da mata masu dauke da juna biyu na shekerar 2024 a garin Bauchi ranar Litinin.
Ya ce an samu rahotan zargin bullar cutar ne a Bauchi da Giade da Toro.
Ya ce “Bamu samu tabbacin wanda ke dauke da cutar Kwalara ba a Bauchi amma mun samu mutane 50 da ake zargin sun kamu da cutar inda mutum guda ya rasu.
” Yakamata mutane su dinga bin matakan kariya na tsaftar muhalli da kuma kai rahotan alamun cutar ga asibiti”.
Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta ce cutar ta amai da gudawa ta bulla a jihohi 30 na kasarnan.
A don haka ne, hukumar ta bukaci gwamnatocin jihohi su dau matakan dakile yaduwar cutar.
