Featured
Yan Bindiga sun nemi Naira Miliyan 900 kudin fansar Mahaifiyar Rarara
‘Yan bindigar da suka sace Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa din nan Dauda Adamu wanda aka fi sani da Rarara, sun nemi a basu Naira Miliyan 900 kudin fansa.
Hakan na zuwa ne kwanaki 6 bayan yin garkuwa da ita.
Wata majiya a zuri’ar gidan dake Kahutu ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun kira su tare da shaida musu cewa suna neman Naira Biliyan 1 kudin fansa.
“Sun kira danginmu da wayar wata mata da suka karba yayin da suka zo daukar Hajiya. Da farko sun nemi Biliyan 1 sai dai bayan tattaunawa sun rage zuwa Miliyan 900.
“Da farko sun nemi tattaunawa da Rarara shi kansa saboda ya kamu da rashin lafiya bayan sace mahaifiyarsa. Sai suka yarda zasu tattauna da wani. Sun tabbatar da cewa Hajiya na cikin koshin lafiya kuma zasu sake ta da zarar an biya kudin”.
Acewar majiyar ‘yan bindigar sun zo da hoton ta ne yayin da suka zo yin garkuwa da ita.
