Featured
Ina da burin horas da tawagar Najeriya ta Super Eagle – Kocin Mali
Kocin kasar Mali, Eric Chelle wanda haifaffen Faransa ne ya bayyana bukatarsa na son horas da Super Eagle ta Najeriya.
Chelle, wanda ya jagoranci tawagar Mali zuwa wasan kusa da na Karshe a gasar kofin Afrika ta bara kuma suka lallasa Najeriya da ci 2 da nema a wasan sada zumunta na kwanan nan ya bayyana bukatar tasa ne yayin wata tattaunawa.
Kocin ya ce babban alfahari da karramawa gare shi a ce yana horas da tawagar Najeriya.
Ya ce Super Eagle na da tarihi mai kyau da gogewa kuma yana da tabbacin zai bada gudunmawa wajen nasararta.
Najeriya dai na fama da kalubale a fannin kwallon kafa tun bayan barin mai horas da Super Eagle, Jose Pesseiro.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya ta nada Finidi George wanda kuma daga bisani aka sallame shi bayan wasanni 2.
Hakan dai ya sanya Super eagle a matsayin kila da wa kala kan damar samun cancantar shiga gasar kofin duniya 2026.
