Featured
Gwamnatin Kano ta bada tallafin magunguna ga makarantun kimiyya a jihar
Domin karfafa kokarin gwamnatin jihar Kano na bunkasa fannin ilimi, hukumar samar da magunguna ta jihar ta bada tallafin maganguna ga kungiyar tsoffin daliban makarantun kimiyya ta KASSOSA don rabawa makarantun kimiyya.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ta DMCSA, Farouk Isa Musa wacce ya fitar a yau Asabar.
Da yake gabatar da gudunmawar magungunan, Darakta janar na hukumar, Pharm. Ghali Sule ya ce hukumar ta bada tallafin ne domin bunkasa fannin iimi a wani mataki na karfafar gwamnatin Abba Kabir Yusuf wacce ta bada muhimmanci a fannin ilimi.
Pharm. Ghali ya ce tallafin zai kasance a matsayin agajin gaggawa ga dalibai kafin a kai su asibiti a yayin da suka kamu da rashin lafiya.
Magungunan da aka bayar sun hada da na zazzabin cizon sauro da na ciwon ciki da sirinji.
A matsayinsa na tsohon shugaban Kungiyar KASSOSA, darakta janar din yayi kira ga makarantun da suka amfana da suyi amfani da maganin ta hanyar da ta dace.
