Featured
Shugabannin Saudia sun taya sabon shugaban kasar Iran murnar lashe zabe
Shugabannin kasar Saudia sun taya murna ga sabon shugaban kasar Iran mai rajin kawo sauyi, Masoud Pezeshkian bayan nasarar lashe zabe da yayi.
Haka kuma sun bayyana fatan karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
A shekarar 2023 ne dai Saudia da Iran wadanda ke ga maciji da juna suka aminta da sake kulla alaka bayan shekaru 7.
Kamfanin dillancin labarai na Saudia SPA ya rawaito Sarki Salman na cewa a shirye suke wajen ci gaba da kulla alaka da Iran don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin duniya.
Haka shi ma Yariman Saudia, Mohammed Bn Salman ya aika da sakon taya murna ga sabon shugaban na Iran.
