Featured
Kungiyar dake kare hakkin masu Auren Jinsi ta fice daga jihar Kano
Mambobin kungiyar nan dake rajin kare hakkin masu auren jinsi a jihar Kano mai suna WISE sun fice daga jihar Kano cikin gaggawa bayan umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf ga hukumar Hisbah na kakkabe ayyukan kungiyar.
Kungiyar ta kuma rufe dukkan shafukanta na Internet bayan shan suka daga al’umma.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce mambobin kungiyar sun bar Kano ne nan take bayan Gwamnatin jihar ta magantu kan ayyukansu.
Majiyar ta shaidawa jaridar PRIME TIME NEWS cewa kungiyar na fargabar abinda ka iya faruwa yayin da al’ummar jihar ke adawa da ayyukansu.
A gefe guda kuma hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce gwamnatin jihar baza ta lamunci ayyukan duk wata kungiya dake koyar da rashin tarbiya ba mussaman batun auren jinsi.
Kwamandan hukumar, Malam Aminu Daurawa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a jiya Litinin.
Hukumar ta kuma bada umarni ga dukkan jami’anta da su guji alaka da duk wata kungiya dake ikirarin taimako har sai sun samu sahalewar shelkwatar hukumar.
