Featured
Tsadar Kayan Abinci: Za a iya samun gagarumar zanga-zanga a Najeriya – Ahmad Lawan
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya ce za a iya samun gagarumar zanga-zanga idan gwamnati bata magance hauhawar farashin kayayyaki da karin kudin wuta ba.
Ahmad Lawan na bayani ne a yayin da yake goyan bayan kudurin da dan majalisa, Sunday Karimi mai wakiltar yammacin Kogi ya gabatar.
Tsohon shugaban majalisar ya ce bai kamata a raina ‘yan Najeriya ba a yayin da ake fama da matsin tattalin arziki.
“Idan bamu dau matakan gaggawa ba kan hauhawar farashin kayan abinci ba da karin kudin wuta, baza mu so muga abinda zai faru kan titina ba”, inji Ahmad Lawan.
” Ba zai yiwu mu dinga rainawa mutane hankali tsawon lokaci ba”.
Tun da farko, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma ya ce farashin kayan abinci ya karu da kaso 300 biyo bayan janye tallafin mai.
“Matsalar tsaro a inda ake samar da abinci da lalacewar hanyoyi da janye tallafin mai na daga cikin ababen da suka sa aka samu hauhawar farashi”, inji.
Majalisar dattawan ta bukaci gwamnati da ta dau mataki kan matsalar.
