Featured
Kotun kolin Najeriya ta dakatar da Gwamnoni daga rike kudaden kananan hukumomi
Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci a karar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnoni 36 na kasarnan kan ‘yancin kananan hukumomi.
A karar da Antoni janar na kasa, Lateef Fagbemi ya shigar ya bukaci a bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kansu da karbar kudadensu kai tsaye.
Sannan gwamnatin tarayyar ta nemi a tilasta yin zabe a kananan hukumomin maimakon nada kantomomin riko.
A hukuncin da mai shari’a, Emmanuel Agim ya yanke, kotun kolin ta ce ya saba da kundin tsarin mulkin kasa yadda kananan hukumomi ke rike kudin kananan hukumomi.
Mai shari’ar ya umarci a dinga mika kudaden kananan hukumomi kai tsaye gare su.
