Featured
Zargin Badakalar Kudade: Kotu taki aminta da bukatar bada umarnin kama Ganduje
Zargin Badakalar Kudade: Kotu taki aminta da bukatar bada umarnin kama Ganduje
Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a, Justice Amina Adamu Aliyu ta yanke hukuncin cewa baza a bada umarnin kamo tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba a shari’ar da ake masa kan zargin badakalar kudade.
Mai shari’ar ta ce duba da yanayin halin da jihar ke ciki yayin da wasu ka iya amfani da lamarin wajen tada zaune tsaye a don haka kotun taki aminta da bukatar sanyawa a kama Gandujen.
Kodayake, mai shari’ar ta ce wanda ake karar wanda ta ce tasan an sadar da shi bayanan karar amma yaki bayyana gabanta za a ci gaba da yi masa shari’a duk da baya kotun.
Mai shari’ar ta kuma nuna bacin ranta kan yadda wadanda ake kara suka gaza bayyana a gaban kotun.
Sai dai lauyan wadanda ake kara, Barista Nuraini Jimoh SAN, ya jadadda cewa kotun bata da hurumin bada wani umarni har sai an saurari kokensa.
Ana karar Ganduje ne da matarsa da karin wasu mutane kan zargin badakalar kudade.
