Featured
Masarautar Kano ta tabbatar da tashin gobara a fadar Sarki dake Kofar Kudu
Masarautar Kano ta tabbatar da samun afkuwar gobara da ake zargin kunnata aka yi a fadar Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na II.
A sanarwar da shugaban ma’aikatan Sarkin Kano, Munnir Sanusi Abbas ya fitar a yau Asabar ya ce wutar ta tashi ne a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce wutar wacce bata yi barna mai yawa ba, ana kan binciken abinda ya haifar da ita.
“Fada na daukar dukkan matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron fada da mutanen dake ciki, kuma tuni aka fara bincike don kaucewa tashin gobarar anan gaba”, inji sanarwar.
