Featured
Dan Fasa Kwauri ya Kashe Jami’in Hukumar Kwastom a Jigawa
Wani dan fasa kwauri ya kashe jami’in hukumar hana fasa kwauri ta kasa dake sashi na 2 na hukumar.
Jami’an ya rasa ransa ne yayin da dan fasa kwaurin ke kokarin kaucewa kamu a garin Achilafia dake titin hanyar Daura zuwa Kano a jihar Jigawa.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na shiyyar hukumar kwastom, Isah Sulaiman ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 12 ga watan Yuli.
Acewarsa, lamarin ya faru ne yayin da motar da ake zargi an yi fasa kwaurinta ne ta afka kan jami’in a kokarin kaucewa kamu.
“An gaggauta kai jami’in asibitin Kazaure daga bisani aka mayar da shi babban asibitin tarayya na Katsina inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. An binne gawar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada”, inji shi.
Shima shugaban sashin hukumar, Kwanturola Ahmadu Shu’aibu a madadin jami’an hukumar ya mika ta’aziyya ga iyalan mamacin.
Kwanturola ya kuma sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu kan lamarin a yayin da aka kama mutum guda da ake zargi.
