Featured
Yanzu-Yanzu: Hadaddiyar Daular Larabawa ta cire haramcin bada biza ga ‘yan Najeriya
Alhaji Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan al’umma ya ce kasar hadaddiyar daular Larabawa ta dage haramcin bada biza ga ‘yan Najeriya.
Ministan ya sanar da hakan ne yayin da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a yau Litinin.
“Kuna sane da cewa Najeriya na tattaunawa da hadaddiyar daular larabawa kan batun bada biza ga ‘yan Najeriya dake son zuwa kasar.
” A yau an cimma yarjejeniya a kan hakan, daga yau 15 ga watan Yuli ‘yan Najeriya zasu iya samun bizar shiga kasar hadaddiyar daular Larabawa”, inji Ministan.
