Featured
Da yiwuwar Tinubu ya mika kudurin dokar mafi karancin albashi mako mai zuwa
Rahotanni na nuni da cewa matukar ba a samu sauyi ba, shugaban kasa Bola Tinubu zai aika kudurin dokar mafi karancin albashi ga majalisar kasa a mako mai kamawa.
Acewar ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, shugaban kasar zai kammala yanke shawara a batun mafi karancin albashin a ranar Alhamis mai zuwa.
Ministan ya bayyana hakan ne a yau Litinin bayan taron majalisar zartarwa ta kasa.
Sannan ya bayyana cewa shugaban kasar zai kuma ganawa da ‘yan kwadago a ranar Alhamis kafin mika kudurin gaban majalisa.
Ya ce majalisar zartarwa ta kasa tattauna kan batun mafi karancin albashin kuma za ta gayyaci kungiyar kwadago a wannan makon.
A makon da ya gabata ne dai shugaban kasar ya gana da shugabannin kwadago kan batun mafi karancin albashin.
