Connect with us

Featured

Ana shirin dakatar da Ndume a majalisar dattawa bayan sukar Tinubu

Sanatocin dake goyan bayan shugaban kasa Tinubu sun fara shirin gabatar da kudurin dakatar da Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu bayan kalaman da yayi na sukar shugaban kasar.

Wasu majiyoyi a majalisa sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, magoya bayan Tinubun na shirin cire Ndume daga mukaminsa bulaliyar majalisar dattawa kuma a dakatar da shi kamar yadda aka yiwa Sanata Abdul Ningi na Bauchi ta tsakiya.

An dakatar da Sanata Ningi ne bayan tattaunawarsa da BBC Hausa inda ya yi zargin cewa ana cushe a kasafin kudin 2024.

A tattaunawar da Ndume yayi da manema labarai a makon da ya gabata ya ce “Shugaban kasa ba shi da masaniyar abinda ke faruwa a wajen fadarsa. An katange shi. Da yawanmu bama iya gana wa da shi”.

” Yanzu sun hana shi yin magana kuma bashi da jami’an hulda da jama’a sai mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, wanda ke rubuta sanarwar manema labarai. ‘Yan Najeriya ransu a bace yake”.

Sai dai bayanan nasa ya jawo ce-ce-ku-ce daga Sanatocin da suke goyan bayan Tinubu ciki har da Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta yamma.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatarwa da jaridar Daily Trust yunkurin dakatar da Ndume daga majalisar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet