Featured
Zamfara: Yan Bindiga sun sace mutane 150 ciki har da jarirai
‘Yan bindiga sun sace mutane 150 ciki har da jarirai a garin Dan Isa na karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara a karshen makon da ya gabata.
Haka kuma an sace wasu mutanen 30 a karamar hukumar Maradun ta jihar.
Acewar wani da ya tsira daga maharan, yan bindigar sun afka garin inda suka kashe mutum 3 tare da sace shanu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar ya ce har yanzu basu samu rahota kan faruwar lamarin ba.
Jihar Zamfara dai ta jima tana fama da kalubalen tsaro na ayyukan ‘yan fashin daji dake garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
