Featured
JAMB ta sanya 140 a matsayin mafi karancin maki don samun gurbin karatu a jami’a
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta sanya maki 140 a matsayin mafi karancin maki domin samun gurbin karatu a jami’a.
Hukumar ta sanya maki 100 a matsayin mafi karanci wajen samun gurbin karatu a kwalejojin fasaha da na ilimi.
Shugaban hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da hakan a yau Alhamis a birnin tarayya Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki a bada gurbin karatu a manyan makarantu na 2024.
Taron ya samu halartar ministan ilimi, Tahir Mamman da shugabbannin jami’o’i da kwalejojin fasaha da na ilimi.
A yayin taron ministan ilimin ya bukaci hukumar JAMB ta bada gurbin karatu ga daliban da suka cika shekaru 18 kadai sai dai mahalarta taron sun ki aminta da hakan abinda ya jawo ministan ya janye umarnin nasa.
