Featured
Kotu ta sanya ranar yanke hukunci ga wanda ya kone masallata a Gezawa
Wata kotun shari’a dake zamanta a Kano a yau Alhamis ta sanya ranar 1 ga watan Agusta domin yanke hukunci a karar da aka shigar da wani mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 kan zargin cinna wuta ga masallata tare da kashe mutane 23.
Ana tuhumar Shafi’u Abubakar da laifin kisan kai da cinna wuta tare da haifar da tashin hankali.
Laifin dai yaci karo da sashi na 140 da na 148 da 167 na dokokin kotun shari’a a Kano.
Tunda farko lauya mai gabatar da kara, Salisu Tahir ya shaidawa kotun cewa ya gabatar da sabuwar tuhuma kan wanda ake karar.
Inda ya bukaci a karanta sabuwar tuhuwamar ga wanda ake karar.
Salishu Tahir yayi zargin cewa a ranar 15 ga watan Mayu da misalin karfe 5:15 na Asuba wanda ake karar ya watsa man fetur tare da kunna wuta a masallacin Larabar Abasawa a karamar hukumar Gezawa inda ya kulle kofa da mutane 23 ciki wadanda suka kone.
Ya ce mutane 23 sun rasu yayin da suke karbar magani a asibitin Murtala.
Wanda ake karar ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.
Lauyar dake kare shi ta bukaci kotun da tayi masa adalci da sassauci tun da har bai wahalar kotun ba.
Daga nan mai shari’a, Halhalatu Zakariyya ya tambayi wanda ake karar ko shin yana cikin hankalinsa yayin da ya amsa laifukan.
Daga nan ya dage zaman kotun zuwa 1 ga watan Agusta don yanke hukunci.
