Featured
CBN ya dawo da siyar da Dalar Amurka ga ‘yan kasuwar canji
Babban bankin Najeriya na CBN ya sanar da dawo da siyar da Dala ga ‘yan kasuwar canji a wani yunkuri na dakatar da faduwar darajar Naira.
Ana canjar da dalar Amurka 1 kan Naira 1, 600 dai a kasuwannin bayen fage.
Siyar da Dalar ga ‘yan kasuwar canjin na zuwa ne watanni 2 bayan siyar da dalar a watan Afrilu.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon Darakta a sashin cinikayya da canji na CBN, A. A Mahdi, babban bankin ya ce zai siyar da Dala dubu 20 ga kowanne dan kasuwar canji.
CBN ya kuma umarci yan kasuwar canjin da su siyar da ita kan Naira 1475.
Bayan sanarwar dai darajar Naira ta daga inda aka canjar da ita kan Naira 1,572 a jiya Alhamis.
