Featured
Marasa kishin kasa ne ke shirya zanga-zanga – Ministan Ayyuka
Gwamnatin tarayya ta bukaci ma’aikata da ‘yan kasa da su karfafa nagartar aiki inda ya ce hakan ne zai inganta rayuwar al’umma a fadin kasar nan.
Ministan ayyuka, Sanata David Umahi ne ya bukaci hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Uburu dake karamar hukumar Ohazora ta jihar Ebonyi.
Mista Umahi yayi bayanin cewa yunwa da ake fama da ita zata kau idan aka koma fannin noma da samar da abinci a cikin gida.
“Yakamata mu fadawa kanmu gaskiya”, inji Umahi.
Dangane da batun zanga-zanga, Ministan ya ce hakan ba alkhairi bane ga kasa.
” Gwamnatin shugaban kasa Tinubu tayiwa mutane aiki. Bari na fada ma ‘yan Najeriyan dake shirin yiwa wannan gwamnati zanga-zanga basa kishin kasa.
“A kan me mutane zasu yi zanga-zanga? Ba don zuwan shugaba Tinubu ba, da muna da kasar da ta gaza ne”, inji shi.
