Featured
Majalisar wakilai ta bukaci a dakatar da shugaban hukumar NMDPRA bayan kalamansa a kan matatar man Dangote
Majalisar wakilai ta tarayya tayi kira da a dakatar da shugaban hukumar kula da harkokin mai ta NMDPR har zuwa lokacin da za a kammala bincike gan zarge zargen da ake yiwa hukumar.
Majalisar ta yi kiran ne bayan amincewa da kudurin gaggawa da Hon. Esosa Iyawe ya gabatar kan neman majalisar ta saurari korafe korafen da suka biyo bayan kalaman shugaban hukumar.
Hon. Iyawe ya shaidawa majalisar cewa ingancin mai na shafar injinan ababen hawa da na masana’antu da kuma fitar da gurbatacciyar iska.
Acewar dan majalisar da ya fito daga jihar Edo, amfani da mai mara kyau na haifar da illa ga lafiyar al’umma.
Kiran na majalisar dai na zuwa ne bayan kalaman, Farouk Ahmed na hukumar NMDPRA kan matatar mai ta Dangote.
‘Yan Najeriya da dama ne suka nemi a kori shi inda suka ce kalaman nasa kashe gwiwa ne ga masu zuba hannun jari a kasar nan.
