Featured
Zanga-zanga: Ministoci da manyan jami’an gwamnati sun shiga ganawar sirri
Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ya shiga ganawa da ministoci a yayin da ake shirin fara zanga-zanga kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya.
Ganawar wacce ke gudana cikin sirri ta samu halartar ministoci sama da 40 na gwamnatin shugaba Tinubu.
Wasu daga cikin ministocin da aka hango a wajen ganawar sun hada da: Nyesom Wike na birnin tarayya Abuja da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da Zephnia Jisalo da Tahir Mamman da Atiku Bagudu.
Sauran ministocin sun hada da Wale Edun na kudi da ministan yada labarai Mohammed Idris da sauransu.
Agefe guda kuma, shugaban kasa Tinubu ya roki matasan Najeriya da su dakata daga shiga zanga zangar ta ‘EndBadGovernance’ da aka tsara farawa a wata mai kamawa.
