Featured
Tinubu Yayi Alla -Wadai Da Kisan Sarkin Gobir
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alla wadai da kisan sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Bawa, kuma ya sha alwashin ɗaukar matakan magance matsalar tsaro a ƙasar.
Shugaban ya yi wannan ta’aziyya ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Ajuri Ngelale.
Sanarwar ta ce: “Shugaba Bola Tinubu ya yi alla-wadai da abubuwan da suka faru waɗanda suka kai ga kisan Sarki Alhaji Isa Bawa.
Shugaban ya kuma bayyana cewa wajibi ne a hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
