Featured
Kotu Ta Bada Belin Ɗan Jarida A Kano
Wata kotun majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, ta bayar da belin wani ɗan jarida a jihar, Wanda ake zargi da wallafa wasu faifan bidiyo na sukar wani hadimin gwamnan jihar.
Tun da fari ’yan sanda sun kama ɗan jaridar mai suna, Mukhtar Dahiru, wanda ma’aikacin gidan Rediyon Pyramid FM ne da ke Kano.
Kan zargin wallafa wani sautin murya da wani ɗan adawa ya zargi Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, cewa yana yaudarar mutane da sunan tausaya musu, bayan kuma almubazzari ne shi.
Alƙaliyar kotun, Mai Shari’a Umma Kurawa, ta bayar da belin dan jaridar kan Naira Miliyan ɗaya, sannan ta ba shi umarnin ya nesanta kansa da wallafa wasu munanan kalamai da za su taɓa mutuncin mai ƙara a shafukansa na sada zumunta.
A karshe ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Oktoba, 2024.
