Featured
Tinubu ya ci amanar mu- Ƙungiyar Ƙwadago
Shugabancin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ya zargi Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da yaudararsu, ta hanyar karya alƙawarin da suka yi tare da ƙara farashin man fetur.
Shugaban NLC Joe Ajaero, ya bayyana rashin jin daɗinsa game halin da ake ciki a Najeriya.
Ajaero, ya bayyana yadda Tinubu ya bai wa NLC da TUC zaɓin su amince da mafi ƙarancin albashin Naira 250,000 tare da ƙara farashin mai, ko kuma su amince da Naira 70,000 amma ba tare da an ƙara farashin man ba.
NLC, ta zaɓi ƙaramin albashin don kaucewa ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin rayuwa.
Sai dai Ajaero ya soki gwamnatin saboda ƙarin farashin mai da aka yi a ranar Talata 03 ga Satumba, 2024. maimakon a barshi a yadda yake kamar yadda aka alƙawarta musu.
Ya bayyana cewar wannan ƙarin zai ƙara jefa ‘yan Najeriya da kasuwanci cikin tsaka mai wuya.
