Featured
Tankar Mai Tayi Ajalin Mutane Sama Da 30 A Neja
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) reshen jihar Neja, ta tabbatar da mutuwar mutane 48, tare da konewar shanu 50, sakamakon hatsarin wata tankar man fetur da ya afku a jiya lahadi a Jihar Neja.
Hakan na kunshe ne, Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Hukumar Abdullah Baba-Arah, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya lahadi 08 ga Satumba, a Minna babban birnin jihar.
Ya ce hukumar ta samu rahoton afkuwar lamarin ne da misalin 12:30 na ranar lahadi, a kan babbar hanyar Bida-Agaie-Lapai.
Baba-Arah, yace lamarin ya faru ne a lokacin da wata tankar mai ta yi karo da wata tirela, wadda ke dauke da matafiya da kuma shanu, Wanda suka taso daga karamar hukumar Wudil ta Jihar Kano zuwa Legas.
A karshe ya tabbatar da mutuwar mutane sama da 30, yayin da Shanu sama da 50 suka kone.
