Featured
Wani Dattijo Ya Rasa Ransa Sakamakon Wanka A Kogi
Wani mutum mai shekaru 55 ya rasu bayan da ya je yin wanka a bakin wani kogi a yankin Hadejia da ke Jihar Jigawa.
Kakakin Rundunar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Jigawa, Badaruddeen Tijjani, ya ce mutumin mai suna Malam Sulaiman Potiskum, dan Shekara 55, ya rasa ransa ne a ranar Asabar 07, ga satumba 2024. A wani rafi da ke yankin Gada Bakin Kogi, a karamar hukumar Hadejia.
Tijjani yace Ajalin ya riske shi ne a lokacin da yake wanka a bakin kogin, amma aka yi rashin sa’a igiyar ruwa ta janye shi, inda daga bisani aka gano gawar sa, kuma babban Asibitin Hadejia suka tabbatar da rasuwar sa.
Jami’in ya ce an miƙa gawar ga iyalan mamacin, sannan ya shawarci masunta da sauran jama’a da su haƙura da zuwa kamun kifi ko wanka a bakin kogi, saboda ƙarfin ruwan, a sakamakon ambaliyar ruwan sama.
