Addini
Ƙungiyar IZALA ta samu sama da naira miliyan 100 a fatun layyar da ta gabata
Ƙungiyar IZALA ta tara kudi kimanin Naira miliyan ɗari da sha biyu ( ₦ 112,000,000.00) wajen tattara fatun layya da jama’a suka taimaka a layyar shekarar 2024/1445H.
Shugaban Kungiyar (IZALA) Sheikh Abdullahi Bala Lau, shine ya sanar da hakan a jiya Asabar 07 ga satumba, 2024. Bayan ya karbi rahoton kwamitin da ya tattara fatun na layya, wanda shugaban kwamitin Malam Lamara Azare ya bayar a garin Dutse dake jihar Jigawa.
Sheikh Bala Lau ya yabawa jama’ar da sukayi hoɓɓasa wajen ganin sun mika fatun layyan su ga kungiyar ta IZALA, ya kuma sha alwashin ci gaba da ayyukan raya addini da kudaden kamar yadda aka saba.
An gabatar da rahoton ayyukan kwamitin a gaban shugabanni da manyan Malaman Ƙungiyar, a taron majalisar ƙasa da ƙungiyar ta gabatar a birnin Dutse dake jihar Jigawa.
Kudaden da aka samu a kowacce jiha su ne :
1.Sokoto ₦14,645,705.00
2.Kaduna ₦12,109,800.00
3.Kebbi ₦11,506,900.00
4.Bauchi ₦ 7,829,582.50
5.Katsina ₦ 7,234,625.00
6.Zamfara ₦6,707,200.00
7.Taraba ₦6,554,825.00
8.Niger ₦ 5,537,800
9.Adamawa ₦5,290,500.00
10.Abuja ₦4,572,250.00
11.Jigawaita ₦3,535,287.50
12.Nasarawa ₦ 3,530,850.00
13.Kano ₦3,330,290.00
14.Gombe ₦ 3,004,100.00
15.Kogi ₦2,952,350.00
16.Lagos ₦2,901,334.00
17.Plateau ₦2,467,350.00
18.Borno ₦2,222,600.00
19.Benue ₦1,295,600.00
20.Kwara ₦1,097,919.00
21.Yobe ₦875,185.00
22.Oyo ₦840,248.30
23.Ogun ₦430,080.00
24.Rivers ₦ 324,450.00
25.Osun ₦287,878.70
26.Delta ₦165,000.00
27.Ondo ₦145,790.00
28.Edo ₦140,000.00
29.Anambra ₦101,000.00
30.Ebonyi ₦83,500.00
31.Akwa Ibom ₦64,100.00
32.Cross Rivers ₦ 53,500.00
33.Enugu ₦53,000.00
34.Abia ₦40,000.00
35.Imo ₦25,000.00
36.Ekiti ₦25,000.00
37.Bayelsa ₦20,000.00
