Connect with us

Featured

Kano: NDLEA ta kama kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogiram miliyan 8.4 a 2024

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta ce ta kama mutane 1,345 da ake zargi, sannan ta kuma kama wasu haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 8,430,239 a shekarar 2024.

Kwamandan Hukumar na jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 02 ga Janairu 2025, yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Kano.

Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 1,301 da mata 44.

Idris-Ahmad, ya ce haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da hemp, hodar iblis, heroin, methamphetamine, codeine, da kwayar tramadol sama da miliyan biyar.

Ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane 128 da aka kama da laifuka daban-daban da suka shafi muggan kwayoyi.

“A wani yunkuri na inganta ayyukan Hukumar, mun kaddamar da ‘Operation Hana Maye’ (Operation Stop Abuse), da nufin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma samar da yanayi mai kyau ga alummar Jihar Kano.

“Mun yi nasarar tarwatsa matattarar yan shaye shaye sama da 20, a wasu fitattun wurare a fadin jihar, kamar Filin Idi, Dan Agundi, Sani Abacha Youth Center, da Sani Abacha Stadium,” in ji Idris-Ahmad.

A cewarsa, hukumar ta gudanar da gwaje-gwajen sahihancin miyagun kwayoyi guda 1,114 ga masu neman takarar zaben kansiloli, domin samar da ingantaccen shugabanci nagari.

Ya kuma ce an yi wa masu shaye-shayen miyagun kwayoyi 101 bita da kuma wayar da kai, ta hanyar shirin gyaran da hukumar ta yi, wanda ya taimaka musu wajen sake shigar da su cikin al’umma.

Idris-Ahmad ya kuma yabawa shugaban hukumar ta NDLEA, Brig. Gen. Mohammed Buba-Marwa, saboda goyon baya da karfafa gwiwa, da kuma gudummawa wajen ganin hukumar ta ci gaba da samun nasarori.

A karshe Kwamandan ya tabbatar da cewa, Hukumar za ta ci gaba da kokarinta, tare da yin amfani da ayyukan leken asiri da hadin gwiwar al’umma don tarwatsa hanyoyin sadarwar muggan kwayoyi da inganta zaman lafiya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet