Connect with us

Featured

Gwamnatin Sokoto ta yi alƙawarin tallafa wa waɗanda gobarar Karar Ƴan Niƙa ta shafa

Gwamnatin Jihar Sokoto ta jajanta tare da yin alkawarin tallafawa wadanda gobara ta shafa a yankin ‘Karar-‘Yan-Nika’ da ke cikin Kasuwar Kara a Sakkwato.

Gobarar wadda ta lalata shaguna sama da 50, ta lalata injinan nika guda 132 tare da cinye kayan abinci masu yawa kamar shinkafa, gero, da wake, inda ta yi sanadiyar asarar miliyoyin naira.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Idris Gobir, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, domin jajantawa wadanda abin ya shafa a madadin gwamnatin jihar.

A yayin ziyarar tasa, ya sanar da kafa kwamitin da zai tantance irin barnar da gobarar ta yi, tare da bayar da shawarar daukar matakan hana faruwar hakan a nan gaba.

Ya kuma tabbatar wa wadanda abin ya shafa cewa, gwamnati za ta dauki matakin gaggawa da zarar kwamitin da aka kafa ya gabatar da sakamakon bincikensa.

Shugaban kungiyar masu nika, Malam Yakubu Bello, ya bayyana alhininsa game da dimbin asarar da su ka yi, inda ya bayyana muhimmancin da injin nikan ke takawa a harkokin yau da kullum na kasuwar.

Hakazalika, shugaban kungiyar matasan ‘yan kasuwa, Alhaji Bashar Nuhu, ya nuna jin dadinsa ga mataimakin gwamnan bisa ziyarar da ya kai masa.

Ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta nuna damuwar gwamnati ga al’ummarta, ya kuma bukaci da a ba su kwakkwaran tallafi, inda ya ce da yawa daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa matasan ‘yan kasuwa ne.

Ita ma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sokoto ta mayar da martani cikin

A nasa bangaren, Mai ba da Shawara na Musamman a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sokoto, Aminu Bodinga, ya yabawa matakan da gwamnati ta dauka, inda ya bayyana ziyarar mataimakin gwamnan a matsayin abinda ya dace.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet