Featured
Hukumar JAMB ta tura sama da Biliyan 50 asusun gwamnatin tarayya a cikin shekaru bakwai
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta (JAMB) ta sanar da tura sama da Naira biliyan 6 zuwa asusun gwamnatin Najeriya a shekarar 2024.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin 06 Janairu 2025, ta hannun mai ba ta shawara kan harkokin sadarwa, Dakta Fabian Benjamin,ya ce, JAMB ta samar da jimillar kudaden shiga na N22,996,653,265.25 a shekarar 2024, wanda daga ciki aka tura Naira 6,034,605,510.69 ga asusun gwamnatin tarayya.
Hukumar ta ce ragin Naira 1,500 na kudin fom na UTME da aka yi wa dalibai, shine ya kara kudin da aka tura zuwa N9,013,068,510.69.
Ya kara da cewa, kudaden sun kasance wani bangare ne na rarar kudaden da suke gudanar da ayyukan su, biyo bayan nasarar gudanar da jarrabawar kammala manyan makarantu na shekarar 2024.
Hukumar ta kuma ce ta bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 50 ga baitul malin Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata a karkashin jagorancin magatakardan hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede.
