Featured
Gwamnatin Bauchi Ta Kori Kwamishinoni Biyar
Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul tare da korar kwamishinoni biyar.
A cewar wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Talata, ta hannun Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da kan Jama’a ’a, Mukhtar Gidado, ya ce an yi wannan sauyi ne domin a inganta harkokin mulki da kuma tabbatar da ingantaccen jagoranci ga alummar jihar.
A cewar sanarwar, a kan haka ne Gwamnan jihar ya sallami kwamishinoni biyar. Wannan matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen shigar da sabbin dabaru a cikin harkokin mulki, wadanda za su yi dai dai da manufofin gwamnan na karfafa gwamnatin sa da kuma magance kalubalen da ke tasowa yadda ya kamata.
“Kwamishinonin da wannan abu ya shafa su ne kwamishiniyar ilimi, Jamila Dahiru, da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Abdulhameed Bununu, kwamishinan yada labarai da sadarwa, Usman Danturaki, kwamishinan noma, Madugu Yalams da kwamishinan harkokin addini, Yakubu Ibrahim.
Gwamna Bala Muhammad ya kuma mika godiyarsa ga kwamishinonin masu barin gado, bisa sadaukar wa da suka nuna, wajen hidima da bayar da gudunmawa mai karfi domin ci gaban Jihar Bauchi.
Gwamnan ya kuma mika sunayen sabbin mutane biyar ga majalisar dokokin jihar domin tabbatar da su a matsayin kwamishinonin.
Sabbin sunayen da aka mika domin maye gurbin sun hada da Babayo Tilde, daga karamar hukumar Toro, Abdullahi Mohammed daga karamar hukumar Misau, Bala Lukshi daga karamar hukumar Dass, Usman Shehu, daga karamar hukumar Shira, Iliyasu Gital daga karamar hukumar Tafawa Balewa, Titus Ketkukah daga karamar hukumar Tafawa Balewa. Babayo Gabarin daga karamar hukumar Darazo, da Lawal Rimin Zayam daga karamar hukumar Toro.”
