Featured
Al-ajabi: Yadda Wani Garin Zip Ya Nutse Gabadaya A Kogin Binuwai
Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai.
Majiyarmu ta ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya hadiye su, sun nutse a cikin ruwa.
Garin na Zip da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido ta Jihar Taraba yana bakin Kogin Biniwai ne, kuma mafi yawan mazaunansa masunta ne da manoma.
Sun kuma bayyana yadda abin ya faru da yadda suka tsallake rijiya da baya da irin asarar da suka tafka da kuma halin da ibtila’in ya jefa su a halin yanzu.
Wani mazaunin garin, Alhaji Gambo Sa’idu, wanda kuma dan uwan sarkin garin ne, ya shaida wa wakilinmu cewa, a gidansa akwai dakuna fiye da takwas kuma gidan nasa kamar sauran gidajen garin duk sun nutse a cikin Kogin Biniwai.
Yadda abin ya faru
Ya kara da cewa tun a shekarun baya ne al’ummar garin suka fara ganin gine-ginen da suke bakin gabar kogin garin sun fara tsagewa, daga bisani wasu suka fara ruftawa suna fadawa cikin kwaryar kogi.
Alhaji Gambo ya ce, “Tsohon Sarkin Zip, Marigayi Alhaji Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba kan yadda gidaje ke ruftawa suna ta fadawa cikin ruwa, amma babu wanda ya zo ya duba abin dake faruwa.”
Babu dauki daga gwamnati
Ya ce, “A can baya lokacin da jama’ar garin suka ga ginegine na tsagewa sarkin garin, Marigayi Uba Sa’idu ya kai rahoto ga Karamar Hukumar Karim-Lamido da kuma Gwamnatin Jihar Taraba har ma da hotuna, amma babu abin da hukumomin Jihar Taraba suka yi har ya zuwa lokacin da garin baki daya ya rufta a cikin ruwa.
“Har zuwa yanzu babu wani jami’in gwamnatin Jihar Taraba ko kuma na Karamar Hukumar Karim-Lamido wanda ya ziyarci garin domin ganin abin da ya faru, kai ma da kanka ka ga inda tsohon garin yake, ruwa da yashi sun rufe garin baki daya, ba wani alamar gini ko bishiya, kuma a yanzu duk al’ummar garinmu a bukoki muke zaune,’’ in ji Ya’u.
Mista Micah Dantala lsoko, wanda shi ne Magatakardan Sarkin Zip, ya shaida wa Aminiya cewa duk gine-ginen da ke garin sun nutse a cikin ruwa wanda haka ya haifar wa da jama’ar garin asarar dukiya mai yawan gaske.
Ya bayyana cewa Masallacin Juma’a da coci da makarantan firamare da asibiti suna daga cikin gine-ginen da suka nutse baki daya a cikin kogin na Biniwai.
Ya ce har yanzu babu wani dauki da aka kawo wa jama’ar garin don tausayawa.
“Mun yi sa’a ba a samu asarar rai a laokacin wannan hadari ba, amma daukacin gine-ginenmu da kayayyakimu duk sun nutse a cikin ruwa yanzu kusan duk al’umma suna zaune tare da iyalansu a dakunan ciyawa domin kayan gini sun yi tsada sosai,’’ in ji Micah.
Shi ma Sarkin garin na Zip, Malam Yusuf Babatato, ya bayyana cewa al’ummar garin sun yi asarar daukacin gidajensu da wuraren kasuwanci da masallatai da coci da makarantar firamare da asibiti.
Ya ce, “Kamar yadda duk wanda ya zo nan zai gani, kusan dukkan jama’a dakunan ciyawa suke zaune tare da iyalinsu.”
