Featured
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Masu Gadin Al’umma Shida A Zamfara
An bayyana cewa an kashe jami’an hukumar kare al’umma ta jihar Zamfara guda shida (CPG) da aka fi sani da Askarawa da wasu ‘yan banga guda hudu a wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Anka ranar Asabar.
Kamar yadda majiyar ta bayyana, jami’an na dawowa ne daga wani sumame da rundunar sojin Najeriya ta yi kuma aka samun nasara, wanda ya yi sanadin kashe ‘yan bindiga da dama.
Sai dai yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa, wasu ’yan bindigar suka yi musu kwanton bauna, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka goma.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da kashe jami’an tsaron a harin kwanton baunar.
A cikin wata sanarwa da ya rubuta cikin harshen Hausa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar, gwamnan ya bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su na cikin tawagar da suka gudanar da wani samame tare da jami’an soji a Anka kafin a kai musu hari a kewayen gadar Bagega.
Gwamna Lawal ya ci gaba da bayyana cewa, wasu ‘yan kungiyar kare hakkin jama’a (CPGs) shida da ‘yan banga hudu da aka fi sani da “Yan Sakai” sun rasa rayukansu a harin.
Ya kara da cewa har yanzu ba a ga mutum uku da suka hada da jami’ai biyu na jami’an tsaro tsaron al’umma da kuma ‘yan banga guda daya.
“Na samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa wasu jami’an tsaro na jihar Zamfara kwanton bauna a karamar hukumar Anka, lamarin ya faru ne a jiya lokacin da jami’an tsaro da jami’an tsaron jihar karkashin jagorancin rundunar sojojin Najeriya suka kai farmaki maboyar ‘yan bindigar inda suka yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama tare da kwato makamansu,” inji shi.
“Bayanan sun bayyana min cewa a hanyarsu ta dawowa ‘yan bindigar sun yi musu kwanton bauna a Bagega tare da bude musu wuta inda suka kashe jami’an tsaron al’ummar Zamfara guda shida (CPG) da Yansakai hudu wadanda aka binne su da safiyar Lahadin nan.
“Akwai mutum uku da suka bace a cikinsu, biyu ‘yan CPG ne, daya kuma Dansakai, da na samu labarin faruwar lamarin, na ba da umarnin a kai agajin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka, sannan kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu za a ba su kayan agajin gaggawa.
“Na yi addu’ar Allah ya karbi rayukan wadanda suka yi sadaukarwa mafi girma domin kare al’ummarsu, Allah ya jikan su, Allah ya kawo mana karshen matsalar tsaro a jihar Zamfara da Arewa da Najeriya baki daya.”
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.
Yayin da aka yi asarar rayuka da dama, da dama sun rasa matsugunansu yayin da ‘yan bindigar ke ci gaba da yin barna a cikin al’umma.
Duk da kokarin jami’an tsaro amma yan bindigar suna ci gaba da kai hare-hare.
