Featured
Gwamnatin Zamfara Ta Amince Da Hutun Haihuwa Na Watanni Shida Ga Ma’aikata Mata
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da bai wa ma’aikatan gwamnati mata hutun haihuwa na watanni shida domin ƙarfafa shayar da jarirai nonon uwa kaɗai da kuma inganta lafiyar uwa da yaro. Shugaban Ma’aikatan Jihar, Yakubu Haidara, ne ya bayyana hakan a Gusau yayin karɓar baƙuncin ƙungiyar CS-SUNN.
Haidara ya ce amincewar Gwamna Dauda Lawal na nuna ƙudirin gwamnatinsa na yaƙi da tamowa a tsakanin yara. Ya bayyana cewa hutun zai bai wa mata damar samun isasshen lokacin murmurewa bayan haihuwa, shayar da jarirai nonon uwa kaɗai da kuma ƙarfafa alaƙar uwa da ɗanta.
Read Also : Tambuwal Ya Buƙaci Ƴan Najeriya Su Tabbatar Sun Kawo Ƙarshen Mulkin Tinubu a 2027
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira miliyan 500 a bara domin shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki. A nasa jawabin, jami’in CS-SUNN, Kabiru Jangeru, ya ce wannan mataki ya yi daidai da shawarwarin UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kan shayar da jarirai nonon uwa na watanni shida na farko.
