Featured
Yara Sama da 500,000 Na Fuskantar Matsananciyar Yunwa a Arewa Maso Yamma – UNICEF
Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta bayyana damuwa kan karuwar matsalar rashin abinci mai gina jiki a arewa maso yammacin Najeriya, inda ta ce sama da yara 500,000 a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa. Wannan bayani ya fito ne bayan gabatar da sakamakon binciken 2025 Nutrition SMART Survey a wani taro da aka gudanar a Sokoto.
Masani a fannin abinci na UNICEF, Edward Kotundo, ya ce binciken ya nuna yawan yara ‘yan kasa da shekara biyar da ke fama da karancin abinci, inda kashi 11 cikin 100 ke fama da matsalar a Sokoto da Kebbi, yayin da Zamfara ke da kashi 8.5. Ya kuma kara da cewa an samu yawan matsalar (stunting) a dukkan jihohin uku, alamar matsalar rashin abinci na dogon lokaci.
UNICEF ta jaddada cewa matsalar ba ta kiwon lafiya kadai ba ce, illa ce ta ci gaba da ke bukatar hadin gwiwar bangarori da dama. Mahalarta taron sun bukaci karin zuba jari da hadin kai domin magance matsalolin da ke haddasa yunwa, ciki har da talauci, rashin wadataccen abinci da kuma karancin samun kulawar lafiya.
