Featured
Ranar Muhalli ta Duniya: Daga Ton Miliyan 4 Na Sharar Roba Da Ake Samu A Najeriya Duk Shekara, A Kano Ake Samar Da Ton Dubu 30
A yayin bikin Ranar Muhalli ta Duniya na shekarar 2025, SFC Training Academy tare da tallafin Partnership for Agile Governance and Climate Engagement (Pace) da hadin gwiwar wasu hukumomi kamar UNICEF, sun hada kan masu ruwa da tsaki a Kano domin tattaunawa kan matsalar karuwar sharar roba, da kuma kawo hanyoyin samar da Muhalli mai inganci.
Taron wanda aka gudanar a yau Alhamis 05 ga Yuni 2025, a Babban dakin taro na Tahir Guest Palace da ke Nassarawa a Jihar Kano. Ya samu halartar masana da masu fashin baki da kuma jami’an gwamnati, inda aka tattaunawa kan dabarun rage sharar robobi da kuma inganta hanyoyin kula da muhalli.
Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, wanda Umar Sani Anka, Daraktan Sauyin Yanayi na Jihar Kano ya wakilta, ya jaddada bukatar haɗin gwiwar al’umma don magance dattin robobi. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta aiwatar da manufofi don rage illolin sauyin yanayi, kuma ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa cibiyar tattalin arzikin zagaye domin samar da ayyukan yi ga al’ummar Kano.
Da ÿake jawabi, wakilin UNICEF, Rahma Muhammad Rahood Farah, ya bayyana goyon bayan hukumar ga gwamnatin Jihar Kano wajen shuka bishiyoyi 100,000 a wasu makarantu kamar GSS Kundila Boys and Girls, GSS Dakatar, da Gama Tudu.
A nasa bangaren, Auwal Hamza, shugaban kungiyar PACE a jihar Kano, ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen sarrafa shara ta hanyar sake amfani da ita, yana mai cewa sarrafa shara nauyi ne da ya rataya akan kowa, kuma yana da kyau a tuna wa kowa mahimmancin samar da tsabtaccen muhalli.
A yayin taron an gudanar da tattaunawa tsakanin masana kan hanyoyin rage sharar roba, da kuma hanyoyin da za a bi dan amfanar ta maimakon barin ta ta zama barazana ga alummah.
Da yake jawabi yayin tattaunawar, Dr. Bello Abba Yakasai, kwararre a fannin kula da shara, ya bayyana cewa sharar roba ta kai matakin ban tsoro a duniya baki ɗaya. Ya ce: “Duniya tana samar da fiye da ton miliyan 400 na roba a kowace shekara, kuma Najeriya kaɗai tana bayar da gudunmawar kusan ton miliyan 4.” Ya ƙara da cewa: “Jihar Kano na samar da kusan ton 30,000 na wannan adadi, wanda hakan ya kasance abin damuwa sosai.”
