Connect with us

Featured

Ƴan Najeriya Ku Ƙara Haƙuri, Sauƙi Na Nan Zuwa – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin ƴan Najeriya da ka da su yanke ƙauna da gwamnatinsa, inda ya ƙara da cewa abubuwan kyautata rayuwarsu na nan tafe ba da jimawa ba.

Tinubu wanda ya yi wannan kiran a saƙonsa na taya Musulmi murnar babbar sallah, ya ce duk da dai tafiyar ba ta rasa kun-kunji amma ya kamata jama’ar Najeriya su ƙara haƙuri.

“Ba lallai mun samu abin da muka so ba amma ina kira ga ƴan Najeriya da ka da su yanke ƙauna. Mu ci gaba da fata mai kyau sannan kuma mu jure. Sauye-sauyenmu da muke son yi na samun haɓaka musamman bisa dogaro da alƙaluman tattalin arziƙi da ke nuna ci gaba. Nan ba da jimawa ba kowa zai kurɓi romon.”

Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan ƙasar su yi wa al’ummar garin Mokwa addu’a sakamakon ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita al’ummar garin bayan kashe mutum kimanin 700.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet