Featured
Ku Guji Bayyana Lambobin NIN Din Ku Domin a Baku Kudi – NIMC
Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa ta Najeriya (NIMC) ta gargadi ‘yan kasar nan da su guji bayyana Lambobin Shaida ta Kasa (NIN) ga wasu da ba su sani ba, ko wasu kungiyoyi domin kawai a basu kuɗi.
Gargadin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, ana yaudarar wasu mazauna Jihar Anambra su bayar da NIN ɗinsu donmin a basu kudi, abinda hukumar ta bayyana a matsayin haramun, kuma laifi ne da za a iya hukunta mutum a karkashin Dokar NIMC mai lamba 23 ta 2007.
A wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Dokta Kayode Adegoke, ya fitar a ranar Laraba 09 ga Afrilu 2025, NIMC ta bayyana cewa an samu rahoto game da wannan haramtacciyar mu’amala, kuma tuni aka kama wasu mutane bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro.
“Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa ta Kasa ta samu rahoton wasu mutane ko kungiyoyi da ba su da izini da ke bukatar mazauna Anambra su mika Lambobin Shaidar su domin samun kuɗi,” in ji sanarwar.
“A kowane lokaci, masu NIN kada su bayar da Lambobinsu don samun kuɗi. Wannan ya saba wa dokokin kasa. Duk wanda aka kama yana yin haka zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji hukumar.
NIMC ta kuma sake nanata gargaɗinta na baya, tana kira ga ‘yan Najeriya da kada su raba NIN ɗinsu ko bayanan su na sirri da wasu da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, saboda hakan na iya jefa su cikin haɗarin satar bayanai da sauran laifukan yanar gizo.Ku Guji Bayyana Lambobin NIN Din Ku Domin a Baku Kudi – NIMC
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoto idan sun ga wani yana tattara NIN ba bisa ka’ida ba, inda ta bukaci ayi gaggawar sanarwa ta shafukan hukumar na yanar gizo.
